TARIHIN HAUSAWA DA BA A FAƊA
Tarihin Da Ba A Fada Na Kasar Hausa Da Hausawa. Kasar Hausa, wadda aka fi sani da Kasar Hausa a harshenmu, wani yanki ne na tarihi a yammacin Afirka da Hausawa ke zaune tun tsawon ƙarnuka. Yankin ya haɗa da arewacin Najeriya da kudancin Nijar. Hausawa na daga cikin manyan kabilu a Afirka, masu ɗimbin tarihi na kasuwanci, shugabanci, ƙere-ƙere, da ilimi. Mafi yawan Hausawa musulmai ne da suke musulunci tun sama da shekara dubu, a cikin Hausawa kuma Akwai mabiya addinin kiristanci da mabiya addinin gargajiya wanda su ke yi tun kafin zuwan Addinan Ibrinayanci(Judaism, kiristanci da musulunci) Asalin Hausawa ya kasance batun muhawara a tsakanin masana tarihi. Wasu masana sun yi imanin cewa Hausawa sun fito ne daga yankunan Habasha, Nubiya, da Masar ta Dauri (Ancient Egypt) bayan ƙaruwar hamada, suka matsa zuwa kudu don kafa sababbin garuruwa. Wani ra’ayi kuma yana danganta Hausawa da gaɓar yammacin tafkin Chadi, inda sauyin yanayi ya tilasta musu bazuwa zuwa yamma, wanda hakan ya haif...